Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Laraba 12 ga watan Yuni a matsayin ranar hutu domin tunawa da ranar dimokuradiyya ta bana.
A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida ta fitar ranar Talata, babban sakatare, Dakta Aishetu Ndayako, a madadin ministan, Olubunmi Tunji-Ojo ya taya ‘yan Najeriya murnar bikin.
A wani bangare an bayyana cewa, “Yayin da muke bikin ranar dimokuradiyya a tarihin kasarmu, bari mu duba mu yi tunani a kan kokarin iyayenmu da suka kafa, mu kuma tabbatar da cewa Najeriya ta ci gaba da kasancewa dunkulalliyar kasa daya kuma amintacciyar kasa da zaman lafiya da kuma rashin rabuwa.”
Karin labari: “Mun daina ɗaukar duk wani labarin da ya shafi gwamnatin Kano” – ‘Yan Jaridun Kano
Sanarwar ta bukaci ‘yan Najeriya da su tsaya tsayin daka kan tsarin mulkin dimokuradiyya.
An yi nuni da cewa, shugaba Bola Tinubu ya himmatu wajen yin gyare-gyare masu kyau don farfado da tattalin arzikin kasa da kuma inganta tsaro.
Sanarwar ta kara da cewa, “Ministan ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da abokanan Najeriya da su yaba da ci gaban da aka samu, da kuma fatan samun makoma mai kyau ga Dimokradiyyar Najeriya.”