An zargi babban sakataren ma’aikatar harkokin wajen tarayya da cin zarafin wata ma’aikaciya

Yusuf, Tuggar, zargi, sakataren, gwamnatin, tarayya
An zargi babban sakataren ma’aikatar harkokin wajen tarayya, Ambasada Ibrahim Adamu Lamuwa da cin zarafin wata ma’aikaciyar ma’aikatar, Simisola Fajemirokun...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

An zargi babban sakataren ma’aikatar harkokin wajen tarayya, Ambasada Ibrahim Adamu Lamuwa da cin zarafin wata ma’aikaciyar ma’aikatar, Simisola Fajemirokun Ajayi.

Ma’aikatar ta aike da karar zuwa ga shugabar ma’aikatan tarayya, Folasade Yemi-Esan, domin yanke hukunci.

Hakan ya biyo bayan wasikar da lauyan Ajayi, Femi Falana, ya aikewa da ministan harkokin waje, Ambassador Yusuf M. Tuggar mai dauke da kwanan watan Mayu 29, 2024.

Karin bayani: Gwamnatin tarayya ta ayyana Laraba a matsayin hutun tunawa da Dimokuradiyyar bana

Koken, wanda Adebayo A. Oniyelu ya sanya wa hannu a madadin Falana, ya bukaci a gudanar da bincike kan zargin cin zarafi dana ofishi da kuma nuna wariya.

Sai dai kwanan wata wasikar da Ambasada Tuggar ya mika wa Yemi-Esan takardar ta sanya rudani a cikin lamarin.

An sabunta ta a ranar 27 ga watan mayu 2024. Amma karar da Ajayi ta shigar, ta hannun lauyanta ya kasance ranar 29 ga watan Mayu, 2024.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here