Hukumar NiMET ta yi hasashen ruwan sama da hadari na tsawon kwanaki uku a fadin Najeriya

Rainfall

Hukumar kula da hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen cewa za a samu yanayi na ruwan sama da hadari a sassan ƙasar daga Litinin zuwa Laraba.

A cikin hasashen yanayi da hukumar ta fitar a ranar Lahadi a birnin Abuja, ta bayyana cewa ana sa ran samun hadari tare da ruwan sama matsakaici a wasu yankunan jihohin Jigawa, Zamfara, Kano, Kaduna, Bauchi, Yobe da Katsina a safiyar Litinin.

Hukumar ta ce daga baya a ranar, ana sa ran samun ruwan sama a jihohin Kebbi, Adamawa da Taraba.

Haka kuma ta yi gargadi cewa akwai yiyuwar samun guguwa da ambaliyar ruwa a wasu yankunan Bauchi, Jigawa, Katsina, Kaduna da Kano a lokacin.

NiMet ta kuma bayyana cewa jihohin kamar su Neja, Binuwai, Babban Birnin Tarayya (FCT), Filato da Nasarawa za su fuskanci yanayi mai hadari da ruwan sama mai sauƙi zuwa matsakaici a safiya, tare da yiwuwar ambaliyar ruwa a wasu sassan Filato.

A kudu, hukumar ta hasashen yanayi ta ce ana sa ran ruwan sama mai sauƙi zuwa matsakaici a jihohin Ondo, Imo, Abia, Enugu, Ebonyi, Anambra, Edo, Delta, Bayelsa, Ribas, Cross River da Akwa Ibom.

A ranar Talata, NiMet ta bayyana cewa arewa za ta yi yanayi mai rana da ɗan gajeren gajimare, yayin da ruwan sama da hadari za su ci gaba da bayyana a wasu sassan Adamawa, Taraba da jihohin makwabtansu.

Hukumar ta kara da cewa a ranar Laraba, ana sa ran yanayi mai rana tare da hadari a yankunan arewa a safiya, yayin da gajimare da ruwan sama matsakaici za su bayyana.

Jihohin kudu irin su Ebonyi, Akwa Ibom, Ribas da Kuros Riba za su samu ruwan sama a safiya sannan daga baya a ranar za a samu ruwan sama mai yawa.

NiMet ta shawarci mazauna yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa da su ɗauki matakan gaggawa, su guji tuƙi lokacin ruwan sama, su tabbatar da an daure kayan da iska ka iya faɗarwa, kuma su kare kansu daga iska mai ƙarfi da sanyi a lokacin dare.

Hukumar ta kuma tunatar da jama’a da su cire na’urorin lantarki daga soket lokacin ruwan sama, kuma su guji tsayawa a ƙarƙashin manyan itatuwa.

Haka kuma, ta bukaci kamfanonin jiragen sama da su nemi cikakkun rahotannin yanayi na filayen jiragen sama kafin tashi ko sauka domin tsaron rayuka.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here