Shugaba Tinubu ya koma Abuja bayan ziyarar aiki a Legas

Tinubu depart US 750x430

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya koma Abuja a ranar Litinin bayan ziyarar aiki ta kwanaki goma da ya kai Legas.

Bayan kammala bikin nadin sabon Olubadan na Ibadanland, Oba Rashidi Adewolu Ladoja, a Jihar Oyo, Shugaban ƙasan ya isa Legas a ranar Juma’a, 26 ga Satumba, inda ya gudanar da taruka da manyan masu zuba jari da suka haɗa da Shugaban Kamfanin Global Infrastructure Partners, Bayo Ogunlesi, da tsohon Shugaban Bankin United Bank for Africa da Etisalat, Keem Belo-Osagie, wanda yanzu shi ne shugaban Metis Capital Partners.

A yayin ziyarar tasa a babban birnin kasuwanci na ƙasar, Tinubu ya karɓi bakuncin Sakatare janar na hukumar kula da harkokin jiragen ruwa ta kasa da kasa (IMO), Arsenio Dominguez, tare da Ministan harkokin jiragen ruwa da harkokin fito Adegboyega Oyetola, da shugabannin hukumomi a fannin.

Shugaban ƙasan ya nanata kudirin gwamnatinsa na inganta harkar ruwa da jigilar kayayyaki a matsayin wata hanya ta maye gurbin dogaro da makamashin man fetur.

A ranar da ta gabaci bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai, Shugaba Tinubu ya ziyarci Jihar Imo, inda ya kaddamar da wasu ayyuka da Gwamna Hope Uzodimma ya aiwatar, tare da gabatar da littafin da gwamnan ya rubuta kan tarihin shekaru 10 na mulkin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Najeriya.

Karin labari: Ziyarar Tinubu jihar Filato ba ta dace ba, rashin tausayi ce – Atiku

Shugaban ƙasan ya kuma gabatar da jawabin bikin ranar ‘yancin kai daga gidan gwamnati na Dodan Barracks, sannan ya kaddamar da sabunta Gidan Wasanni na Ƙasa wanda yanzu aka sake masa suna Cibiyar Al’adu da Fasaha ta Wole Soyinka, inda ya yi kira ga ‘yan ƙasa su rika faɗar alheri game da ƙasarsu.

A ranar Asabar, 4 ga Oktoba, Shugaba Tinubu ya ziyarci garin Jos, babban birnin Jihar Filato, daga Legas domin halartar jana’izar Mama Lydia Yilwatda, mahaifiyar Farfesa Nantawe Yilwatda, shugaban jam’iyyar APC.

A wajen jana’izar, Shugaban ƙasan ya nuna girmamawa ga marigayiyar ya tabbatar wa al’ummomin Kirista na Arewacin Najeriya da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tabbatar da adalci da daidaito tsakanin addinai a ƙasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here