Gwamnatin tarayya ta naɗa babban Akanta na riƙo

Ahmed Zainab
Ahmed Zainab

Gwamnatin tarayya, ta amince da naɗin Mista Anamekwe Chukwunyere Nwabuoku a matsayin mai kula da ofishin Akanta Janar na Tarayya biyo bayan binciken da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ke yi ga dakataccen Babban Akanta Janar na Ahmed Idris bisa zarginsa da almundahanar kudi.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 20 ga wannan wata da muke ciki na Mayu mai sa hannun Aliyu Ahmed, Babban Sakataren ma’aikatar Kuɗi, Kasafin da Tsare-tsare ta ƙasa.

A wannan matsayi dai ana sa ran Mista Anamekwe zai gudanar da aikinsa bisa bin dokoki da ƙa’idojin da suka kuma bisa nuna Cikakkiyar ƙwarewarsa.

Mista Anamekwe yana da babbar Difuloma watau HND a fannin aikin akanta da ya karanta a jami’ar IMT da take a birnin Enugu tare da shaidar digiri na biyu da a fannin sarrafa kudi da ya karanta a jami’ar Common Wealth da ke Belize.

Ya fara aikinsa na farar hula da Cibiyar Nazarin Dimokuraɗiyya CDS kuma ya kai matsayin Babban Akanta tsakanin 1992 zuwa 1995.

Mista Anamekwe, wanda ya halarci kwasa-kwasan gudanarwa da dama a gida da waje, kuma mamba ne a ƙungiyar ƙwararrun akantoci ta Najeriya ICAN, sannan kuma ɗan ƙungiyar ƙwararrun masana tattara kuɗaɗen haraji ne watau CITN, kuma mamba a cibiyar harkokin gudanarwa ta Najeriya NIM.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here