Amnesty ta bukaci a gudanar da bincike kan zargin cin zarafin mace da ake yi wa Sarkin Daura

Facebook 1795365537296 7530308854545750995 750x430

Kungiyar Amnesty International ta bukaci gwamnatin jihar Katsina da rundunar ‘yan sandan Najeriya da su gudanar da bincike cikin gaggawa kuma mai inganci kan zargin cin zarafin wata mata ‘yar yawon bude ido da ake yi wa Sarkin Daura mai shekaru 92, Faruk Umar Faruk.

SolaceBase ta ruwaito cewa kungiyar kare hakkin bil’adaman ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi cewa lamarin, wanda ya faru a ranar 14 ga Nuwamba, lokacin da wata mata ‘yar kasar Poland ke ziyartar fadar Sarkin Daura da ke jihar Katsina, abin damuwa ne matuka.

Faruk Umar Faruk ya zama Sarkin Daura na 60 a watan Fabrairun 2007.

“Bidiyoyin da suka yadu a kafafen sada zumunta, wanda wadda ta ce an ci zarafinta ta wallafa, sun nuna yadda Sarkin ya yi kokarin lalata da ita ta hanyoyi daban-daban, duk da cewa tana nuna rashin amincewarta. Matar ta yi zargin cewa Sarkin Daura ya taba jikinta ta hanyoyi da dama da ba su dace ba,” in ji sanarwar.

“Mun yi kakkausar suka ga wannan mummunan hali na cin zarafi.

“Ya kamata gwamnatin jihar Katsina da rundunar ‘yan sandan Najeriya su gudanar da bincike mai zaman kansa, na gaskiya kuma a bayyane, domin tabbatar da cewa an hukunta Sarkin bisa zargin yunkurin yi mata fyade, ta hanyar shari’a mai adalci, ba tare da hukuncin kisa ba.

“Wannan mummunan lamari dama ce ga gwamnati ta tabbatar da cewa a Najeriya babu wanda ya fi karfin doka.

“Lamarin ya nuna yadda ake mayar da fyade da cin zarafin mata tamkar abubuwan da suka zama ruwan dare, tare da aikata su ba tare da hukunci ba.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here