Wata jami’a ta kori malamai 3 kan zargin lalata

LASU

Hukumar gudanarwar Jami’ar kimiyya da fasaha ta jihar Legas (LASUSTECH) ta kori malaman jami’o’i uku bisa zargin lalata.

Malaman uku da aka kora sun hada da Nurudeen Hassan daga sashin koyar da harkokin sadarwa, da Kareem Arigbabu da Olayinka Uthman daga sashin fasaha da zane zane.

Takardar korar mai taken: “Korar ma’aikata saboda zargin lalata”. Ta ce an yanke shawarar korar malaman ne bayan tattaunawa da majalisar gudanarwar cibiyar kuma hukuncin ya yi daidai da sashe na 5.5.2(v) na sharuddan hukunta manyan ma’aikatan jami’ar.

Jami’in hulda da jama’a na jami’ar Olanrewaju Kuye, ya tabbatar da korar da aka yi ga manema labarai, inda ya ce kwamitin ladabtarwa na jami’ar ne ya yanke hukuncin.

Karanta: Jami’ar KHAIRUN ta yi bikin rantsar da sabbin dalibai sama da 570

“Gaskiya ne su uku an sallame su, Majalisar gudanarwa ta bi dukkan matakai, mun yi musu tambayoyi kafin a kore su,” inji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here