Gwamnatin jihar Kwara ta tabbatar da bullar cutar monkeypox a jihar.
Bayanin bullar cutar na dauke cikin wata sanarwa da kwamishinan lafiya na jihar, Dr Raji Razaq ya fitar yau Litinin a Ilorin.
Sanarwwar tace tabbatar da gani bular cetar ya biyu bayan kokarin su na sa idon da bin diddigi akan cutar, tun daga samu bullar cutar a Najeriya a watan March 2022.
Sanarwar ta kara da cewa wanda yake dauke da cutar na karbar kulawar gaggawa a asibi, sanan kuma jami’an lafiya na jihar na bin diggin wadan da yai mu’amula dasu, domin dakile cutar.










































