Hukumar lafiya ta Duniya, WHO, ta ce sama da mutane 700,000 ne ke kashe kansu a duk shekara a faɗin duniya, inda kashi 77 cikin 100 na kashe-kashen na duniya ke faruwa a kasashe masu karamin karfi da matsakaita.
Wakilin WHO a Najeriya, Walter Kazadi Mulombo ne ya bayyana hakan a jiya Lahadi cikin wata sanarwa da ya fitar domin bikin ranar rigakafin kashe kai ta duniya ta bana.
A cewarsa, ga kowane kashe kai, akwai yiwuwar wasu mutane 20 da ke yin yunƙurin kashe kansu kuma da yawa suna da tunanin kashe kan na su.
“Kisan kai shi ne na huɗu da ke haddasa mace-mace tsakanin ‘yan shekara 15-29. Duk wani lamari na kashe kai bala’i ne da ya shafi iyalai da al’ummomi da kuma ɗaukacin ƙasar, kuma yana da tasiri mai dorewa a kan mutanen da aka bari a baya” Inji shi.
Mulombo ya ce ana iya magance kashe kai ta hanyar lokaci, ganin yunkurik kisan da ido da kuma hanyoyin kariya marasa cin kuɗi.













































