Tinubu ya tafi Landan

73D00AB0 1886 4B4D 8FF2 A0CEC95264F5
73D00AB0 1886 4B4D 8FF2 A0CEC95264F5

Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu ya fita kasar waje bayan shafe makonni yana tattaunawa da masu ruwa da tsaki a kasar kan kudirin sa na shugaban kasa a 2023.

Wata majiya a sansanin tsohon gwamnan jihar Legas ta tabbatar wa TheCable, a ranar Juma’a, cewa Tinubu ya tafi Landan, Birtaniya, “don ganin iyalinsa”.

Wasu majiyoyi sun ce jigon na APC ya fita ne daga kasar domin ya huta tare da ganin likitocinsa.

Wannan na zuwa ne kasa da watanni

4 bayan da Tinubu ya dawo Najeriya daga balaguron jinya na tsawon watanni uku zuwa kasar Burtaniya inda aka ce an yi masa tiyata a gwiwa.

Bayan wata guda, ya ziyarci shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu, a gidansa dake babban birnin tarayya (FCT) inda suka yi ganawar sirri.

Kwanan nan ne tsohon gwamnan Legas ya ziyarci jihar Oyo kan rasuwar Jimoh Oyewumi, Soun Ogbomoso; Saliu Adetunji, Olubadan na Ibadanland, da Alao-Akala, tsohon gwamnan Oyo.

Ya kuma gana da Seyi Makinde, gwamnan jihar a Ibadan.

A ranar 20 ga watan Janairu, ya kuma kai ziyara Minna, babban birnin jihar Neja, domin tuntubar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), tsohon shugaban mulkin soja.

Tinubu dai bai halarci taron kaddamar da kwamitocin aiki na kungiyar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu (ABAT) ba a Legas ranar Alhamis.

Da yake jawabi yayin taron, gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana jigon jam’iyyar APC a matsayin wanda ya fi cancantar maye shugaba Buhari, kuma mafi cancantar zabar shugaban kasa a 2023.

A farkon watan ne Tinubu ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Tsohon gwamnan na Legas ya bayyana yunkurinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa a matsayin wani buri na rayuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here