Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, ya kai ziyarar girmamawa ga shugaban ƙasar Ghana, John Dramani Mahama, a fadar gwamnati da ke Accra, inda suka sake jaddada dangantakar da ta daɗe tsakanin Najeriya da Ghana tare da tattauna batutuwan tattalin arziki da tsaro da suka shafi yammacin Afirka.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa a yayin ganawar, Sarkin Kano ya tuna haɗuwarsu ta farko a lokacin rikicin kuɗi na duniya, lokacin da dukkansu ke rike da manyan muƙaman gwamnati a kasashensu, inda shi ya kasance gwamnan babban bankin Najeriya, yayin da Mahama ke rike da mukamin mataimakin shugaban ƙasar Ghana.
Sarkin ya bayyana cewa a wancan lokaci ya je Ghana cikin gaggawa domin kwantar da hankula kan tsaron bankunan Ghana, bayan tashin hankalin da ya biyo bayan fallasar bankunan Najeriya da ke aiki a ƙasar, yana mai cewa daga nan ne dangantakarsu ta fara a matakin aiki.
Ya ƙara da cewa sun sake haɗuwa a wasu lokuta daga baya, ciki har da bayan rasuwar tsohon shugaban ƙasar Ghana John Atta Mills, lokacin da Mahama ya karɓi mulkin ƙasa a matsayin shugaban ƙasa, abin da ya ƙara ƙarfafa alakar su.
Sarkin Kano ya bayyana cewa babban dalilin ziyararsa a wannan karo shi ne taya Mahama murna kan nasarar zaɓensa na baya-bayan nan, tare da yaba masa kan rawar da yake takawa wajen jagoranci a yankin yammacin Afirka, yana mai jaddada cewa Ghana na da muhimmanci a zuciyarsa.
A nasa bangaren, shugaban ƙasar Ghana John Dramani Mahama ya yi bayani kan yadda tattalin arzikin ƙasarsa ke farfaɗowa, har ma ya ce an samu daidaito bayan sake fasalin basussuka, kudin ƙasar ya ƙarfafa, sannan hauhawar farashi ta ragu sosai, tare da bayyana buƙatar haɗin gwiwar kasashen yankin wajen tinkarar matsalolin tsaro a yankin Sahel.
Mahama ya yaba da irin gudunmawar da Sarkin Kano ya bayar a baya a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya, ta hanyar matakan da ya ɗauka wanda suka taimaka wajen dawo da kwarin gwiwa a harkar bankuna, tare da ɗora harsashin ƙarfinsu a faɗin Afirka, sannan ya nuna fatan zai sake kai ziyara birnin Kano nan gaba













































