Majalisar Dattawa ta tabbatar da Mohammed da Eyesan a matsayin shugabannin hukumomin NMDPRA da NUPRC

Senate (1)

Majalisar Dattawan Najeriya ta tabbatar da naɗin Saidu Mohammed da Oritsemeyiwa Eyesan a matsayin manyan shugabannin hukumomin kula da harkar man fetur na ƙasa.

Oritsemeyiwa Eyesan an tabbatar da shi a matsayin babban daraktan hukumar kula da hakar man fetur ta ƙasa NUPRC.

Haka kuma, majalisar ta tabbatar da Saidu Mohammed a matsayin babban daraktan hukumar kula da man fetur ta ɓangaren da kayyade farashi NMDPRA.

Karin labari: A gaggauce: Farouk Ahmed da Gbenga Komolafe sun yi murabus, Tinubu ya miƙa sunayen waɗanda za su maye gurbin su ga Majalisar Dattawa domin tantancewa

Tabbatarwar ta biyo bayan nazari da amincewa da rahoton kwamitin haɗin gwiwa na majalisar dattawa kan harkokin man fetur na ɓangaren sama, ɓangaren ƙasa da gas.

Kwamitin ne ya gudanar da tantancewa da bincike kan waɗanda aka zaɓa kafin miƙa rahotonsa ga majalisar dattawa domin yanke shawara.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa majalisar dattawa ta amince da rahoton kwamitin baki ɗaya, lamarin da ya kai ga tabbatar da naɗin Mohammed da Eyesan a matsayin shugabannin hukumomin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here