Tsofaffin ‘yan majalisar tarayya sun goyi bayan wa’adin Tinubu na biyu, sun amince Barau a matsayin gwamnan Kano

WhatsApp Image 2025 12 19 at 15.10.32 750x430

Wasu tsofaffin ‘yan majalisar tarayya daga jihar Kano sun nuna goyon bayansu ga wa’adin mulki na biyu na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tare da amincewa da Mataimakin Shugaban Majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, a matsayin ɗan takarar gwamnan Kano.

Tsofaffin ‘yan majalisar, waɗanda suka yi aiki a jamhuriyoyi ta biyu, ta uku da ta huɗu, sun bayyana wannan matsaya ne yayin ziyarar girmamawa da suka kai wa Mataimakin Shugaban Majalisar dattawa a Abuja.

Ƙungiyar, ƙarƙashin jagorancin Hon Umar Sadiq wanda ya wakilci mazaɓar Kumbotso a majalisar tarayya tsakanin shekarun baya, ta bayyana cewa yanke shawarar goyon bayan Shugaba Tinubu da Sanata Barau ya samu amincewar dukkan mambobin ƙungiyar ba tare da sabani ba.

Mai bai wa Mataimakin Shugaban Majalisar dattawa shawara kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Malam Ismail Mudashir, ya bayyana cewa tsofaffin ‘yan majalisar sun kuduri aniyar wayar da kai da kuma tunkarar al’umma domin tabbatar da burin wa’adin mulki na biyu na Shugaba Tinubu da kuma anfanin Sanata Barau na tsayawa takarar gwamnan Kano.

Karanta: Zaɓen gwamnan Kano 2027: Tsoffin shugabannin ƙananan hukumomi sun mara baya ga Sanata Barau a matsayin ɗan takarar APC kaɗai

Ƙungiyar ta jaddada cewa ba ta da wani ɗan takara daban face Sanata Barau, tana mai bayyana shi a matsayin ginshiƙin ƙungiyarsu kuma ɗaya daga cikin fitattun ‘yan siyasar Kano, tare da nuna gamsuwa da ayyukan da yake yi wanda suka ce ya yi daidai da abin da ake tsammani daga gwamna.

Wasu daga cikin tsofaffin ‘yan majalisar sun bayyana Sanata Barau a matsayin albarka ga al’ummar Kano da kuma jam’iyyar APC, suna mai cewa nasarorin jam’iyyar a jihar na da alaƙa da rawar da yake takawa a harkokin siyasa da ci gaban al’umma.

A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Majalisar dattawa, Sanata Barau, ya gode wa tsofaffin ‘yan majalisar, yana mai bayyana su a matsayin tubalin siyasar Kano, tare da jaddada cewa manufarsu ita ce ceto jihar daga halin da take ciki, da kuma haɗa ƙarfi da ƙarfe domin tabbatar da ci gaba da amfani da albarkatu wajen amfanin kowa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here