Jami’ar Amurka Ta Tabbatar Da Tinubu Ya Yi karatu a jami’ar, Ya Kuma Kammala Karatunsa A Shekarar 1979

BolaTinubuChicagoStateUniversityClassPhoto 708x430
BolaTinubuChicagoStateUniversityClassPhoto 708x430

Jami’ar Jihar Chicago (CSU), a jiya, ta tabbatar da cewa, Shugaba Bola Tinubu ya halarci jami’ar kuma ya kammala karatunsa a shekarar 1979 da digirin farko.

Jami’ar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka bayar ga CBS Broadcasting Inc. wanda aka fi sani da CBS News, daya daga cikin manyan gadin jaridun Amurka kuma mafi tasiri.

Duk da haka  jami’ar tace, tarayya ta Amurka, ta hana su samar da wani ƙarin bayani game da rikodin Tinubu, ba tare da izini ba ko sai dai idan an ba da izinin yin haka ta hanyar kotu.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa takardun da ke nuna cewa Tinubu ya kammala karatunsa ne daga jihar Chicago a 1979, ba sahihai ba ne, kuma ya bayyana hakan a matsayin hujjar soke nasarar zaben Tinubu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here