Wasu fusatattun matasa sun kona makarantar Noble Kids Academy da ke Kano saboda sace dalibar ‘yar shekara biyar mai suna Hanifa Abubakar da malaminta ya yi.
Solacebase ta ruwaito cewa mamallakin makarantar Abdulmalik Tanko ya yi garkuwa da dalibar tasa tare da kashe ta duk da karbar kudin fansa.
Shiga nan domin kallon Bidiyon
A wannan faifan bidiyon da kuka gani, ginin makarantar ne ci tsaka da ci da wuta da tsakar daren Lahadi.
Gwamnatin jihar Kano ta bayar da umarnin rufe makarantar ba tare da bata lokaci ba, biyo bayan kama mamallakin makarantar.
An dai yi ta cece-ku-ce kan kisan, inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da tabbacin cewa za a yi adalci a kan wadanda suka aikata laifin.













































