Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta fitar da sunayen wadanda suka gaza sabunta takardun filayensu a ci gaba da aikin sake tantance filaye a jihar.
Kwamishinan filaye da tsare-tsare na jihar, Alhaji AbdulJabbar Garko ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar Talata.
Ya ce baya ga jaridun na kasa, za a buga sunayen wadanda suka gaza a dakin karatu na jihar Kano, Sakatariyar Audu Bako, Gidan Murtala da kuma Babbar Kotun Jihar Kano, domin a sanar da daukar matakin da ya dace.
Ya sanar da tsawaita wa’adin sake tantancewa nan da kwanaki 60 don baiwa masu mallakar filayen da ba su sake sabunta takardun su ba dontantancewa.
Kwamishinan ya kuma ce ma’aikatar ta samu nasarar tantance kadarori 241,025 a cikin kananan hukumomin Nassarawa da Fagge.
Ya ce sun dade suna tantance kadarorin a fadin kananan hukumomin Tarauni, Dala, Karamar hukumar birni da Gwale. (NAN)