Tsohon babban hafsan sojin Najeriya Janar Christopher Musa ya bayyana cewa babu wasu ƙasashe da suke da ikon magance matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta, yana mai jaddada cewa dole ne ‘yan Nijeriya su ɗauki alhakin dawo da zaman lafiya a ƙasar.
Musa ya yi wannan batu ne a wani taron al’adu da ƙungiyar hadin kan tsoffin ɗalibai ta shirya a Abuja domin ƙarfafa haɗin kai da nuna bambancin al’adu.
Taron ya zama dandamali na nuna yadda al’ummar ƙasar ke da yalwar al’adu da kuma yadda irin wannan haɗuwa ke ƙara tabbatar da yiwuwar samun cikakken haɗin kai a tsakanin mutanen ƙasar muddin aka rungumi zumunci da fahimtar juna.
Musa ya bayyana cewa nuna al’adun da aka yi a wajen taron ya nuni da cewa ana iya samun haɗin kai na gaskiya tsakanin kowa da kowa idan aka yarda da bambance-bambance.
Tsohon hafsan sojin ya yi kira ga ‘yan ƙasa da su guje wa duk wani abu da zai rarraba su, tare da ƙarfafa kaunar juna da ƙasar baki ɗaya.
Ya jaddada cewa al’umma na da babban nauyi na gina zaman lafiya ta hanyar rungumar juna da kuma bayar da gudunmawar da za ta tabbatar da dawwamar haɗin kai.
A wani ɓangare na jawabinsa game da maganganun shugaban ƙasar Amurka Donald Trump kan yiwuwar matakin soja a kan Nijeriya, Musa ya nuna cewa kare ƙasa aikinsu ne mutanen da suka fito daga cikinta, domin babu wata ƙasa ta waje da za ta zo ta magance musu matsalolin da suke da alhakin warwarewa da kansu.
Shugaban ƙungiyar usosa Michael Magaji ya bayyana cewa ƙungiyar na da tarihin riƙe da amanar haɗa al’ummar ƙasa tun bayan samuwar makarantun unity, waɗanda aka kafa domin haɗa matasa daga sassa daban-daban na ƙasar a wuri guda domin gina fahimtar juna da jagoranci mai inganci.
Ya ce ƙudurin waɗannan makarantu tun farko shi ne haɓaka tarbiyya da natsuwa tsakanin matasa masu fitowa daga yankuna daban-daban.
Magaji ya bayyana cewa shirin makarantun unity ya taimaka wajen samar da shugabanni a fannoni daban-daban ciki har da siyasa, tsaro, kasuwanci da wasanni, yana mai cewa tsarin ya ba da babban gudunmawa wajen gina al’ummar da ke mutunta juna.
Shugaban tawagar usosans a Abuja Nnanna Anyim Udo ya bayyana ƙungiyar a matsayin masu kula da muhimmin aikin ƙasa, inda ya ce makarantu unity an gina su ne domin samar da muhalli mai cike da al’adu, harsuna da addinai daban-daban domin haɓaka zaman tare da daraja kishin ƙasa.
Ya kuma jaddada cewa ƙungiyar za ta ci gaba da kasancewa hanyar yakar abinda ke rura ƙiyayya da rarrabuwar kai musamman a tsakanin matasa ta hanyar inganta fahimtar juna.













































