DA DUMI-DUMI: Matar tsohon gwamnan Obiano, Ebelechukwu, ta mari Bianca Ojukwu a wajen bikin rantsar da Soludo

L R Ebelechukwu Obiano and Bianca Ojukwu
L R Ebelechukwu Obiano and Bianca Ojukwu

An dan samu wani hargitsi ranar Alhamis a wurin bikin rantsar da Farfesa Chukwuma Soludo a matsayin gwamnan Anambra lokacin da uwargidan gwamna mai barin gado Willie Obiano ta mari Misis Bianca Ojukwu a wajen taron.

Wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN da ke wajen taron ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne bayan an rantsar da Soludo.

Rohtanni sun bayyana cewa wasu daga cikin manyan baki da suka hada da tsohon gwamna Obiano sun riga sun zauna lokacin da matar Obiano ta shigo ta kuma zarce a layin gaba inda matar Dim Odumegwu Ojukwu ta zauna tare da dalla mata mari.

Wannan lamari yaja hankali jami’an tsaro da wasu mutane, inda suka janye Misis Obiano daga hannun Bianca wadda ta yi matukar kaduwa da lamarin.

Daga baya an tafi da matar Obiano, kuma jim kadan, mijin nata ya bar wurin bayan an rantsar da sabon gwamnan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here