Majalisar Wakilai Ta Nemi FG Ta Hana Amfani Da littafin karatun yara, Queen Premier

Books 750x430
Books 750x430

Majalisar Wakilai Ta Nemi FG Ta Hana Amfani Da littafin karatun yara, Queen Premier

Majalisar wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya da sauran kananan hukumomi da su haramta amfani da wani shahararren littafin karatun yara mai suna “Queen Premier” a makarantun kasar.

‘Yan majalisar sun bukaci gwamnatin tarayya da jihohi da kananan hukumomi da su hana littafin saboda ya kunshi kalmomi kamar “gay” da “eros” da sauran su da ake ganin “batsa”.

Kiran haramcin ya biyo bayan amincewa da kudirin da Sulaiman Gumi (PDP, Zamfara) ya gabatar a ranar Alhamis yayin zaman majalisar.

Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa a kwanakin baya ne gwamnatin jihar Kano ta haramta  amfani da littattafan a dukkan makarantun da ke jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here