Ƙungiyar kiristocin Najeriya ta jihar Niger ta tabbatar da cewa an sace jimillar dalibai da malamai 227 daga makarantar firamare da sakandaren St. Mary’s catholic da ke Papiri.
Shugaban ƙungiyar kiristocin Najeriya na jihar, wanda shi ne limamin cocin catholic a Kontagora mai kula da yankin Papiri, ya bayyana cewa cikin waɗanda aka sace akwai dalibai 215 da malamai 12.
Ya ce ya kai ziyara ƙauyen da daren da abin ya faru domin ganin makarantar da iyayen yaran tare da tabbatar musu cewa ana aiki tare da gwamnati da jami’an tsaro domin ceto yaran cikin koshin lafiya.
Ya bayyana cewa lokacin harin ’yan ta’adda wasu daliban sun tsere, kuma wasu iyaye sun fara karɓar yaransu domin makarantar ta rufe gaba ɗaya bayan faruwar lamarin.
Labari mai alaƙa: Gwamnatin Jihar Neja ta tabbatar da sace ɗalibai, ta zargi makarantar da rashin bin umarnin tsaro
Duk da haka, gwamnatin jihar da jami’an tsaro ba su fitar da cikakken bayani kan adadin mutanen da aka sace tun bayan aukuwar harin ba.
Lamarin ya haifar da fargaba a yankin yayin da al’umma ke sake kira ga hukumomi da su dauki matakin gaggawa wajen kare makarantu da tabbatar da tsaro ga ɗalibai.












































