Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Nasiru Baballe Ila a matsayin babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin majalisar wakilai ta kasa.
A wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Garba Shehu, ya sanyawa hannu a daren Lahadi ta ce Ila ya maye gurbin Umar Ibrahim El-Yakub wanda aka nada karamin ministan ayyuka da gidaje tun a ranar 6 ga watan Yulin da muke ciki.
Sanarwar mai taken ‘Shugaba Buhari ya nada Honorable Nasiru Ila, a matsayin babban mai taimakawa kan harkokin majalisun kasa.’
Ta bayyana cewa: “Hon Nasiru, wanda ya fito daga Makarantun Victory College, da Alexandria and West London College, dake Kasar Burtaniya, ya kasance hamshakin dan kasuwa ne mai safarar kayan masarufi da sana’ar fata kafin ya shiga harkokin siyasa.

“A shekarar 2011 da 2015, an zabe shi a matsayin dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Tarauni a Kano.”
Har ila yau Ila mamba ne na kungiyar Akantoci ta kasa wato Association of National Chartered Accountants of Nigeria.













































