Bamise : Kotu ta tsare direban BRT 

Bamise1
Bamise1

Wata kotun Majistare da ke Yaba a Legas ta bayar da umarnin tsare wani direban motar Bus Rapid Transit (BRT) Mista Andrew Nice na tsawon kwanaki 30 bisa zarginsa da hannu a mutuwar fasinjansa, Oluwabamise Ayanwole.

Kotun ta bayar da umarnin ne biyo bayan bukatar da ‘yan sandan suka yi, a ranar Juma’a.

Lauyan ‘yan sanda, Yetunde Cardoso, wanda ya shigar da karar ya shigar da karar ne kan tuhume-tuhume hudu da suka hada da kisan kai, cin zarafi, rashin da’a da kuma kutse ga gawa.

An tsinci gawar Bamise, mai shekaru 22 a ranar Litinin da ta gabata a kan gadar Carter, Legas Island – kwanaki tara bayan an bayyana bacewar ta bayan ta hau motar Nice.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here