Ganawar da aka yi tsakanin zababben shugaban kasa, Bola Tinubu da Rabiu Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP na ci gaba da tayar da kura, musamman a tsakanin shugabannin jam’iyyar APC mai mulki a Kano.
Rahotanni sun bayyana yadda Tinubu da Kwankwaso suka gana na tsawon sa’o’i hudu a kasar Faransa, inda suka tattauna batutuwa da dama da suka hada da yiwuwar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP ya shiga majalisar ministoci mai jiran gado.
Da yake mayar da martani, Abdulmajid Kwamanda, wani jigo a jam’iyyar APC a Kano, ya ce bai kamata Tinubu ya bai wa Kwankwaso wani mukami, ko da kuwa dan aike ne.
“Mu a Arewa maso Yamma ba ma maraba da Rabiu Musa Kwankwaso zuwa jam’iyyar mu ta APC. Ba mu yarda da ra’ayin Bola Tinubu ya ba shi wani mukami ba ko da kuwa a matsayin dan aike ne a jam’iyyarmu mai daraja. Idan Tinubu ya yi watsi da kukanmu ya nada Kwankwaso, to babu shakka za mu tarwatsa jam’iyyar APC ta Arewa baki daya, mu janye goyon bayanmu gare shi,” inji Kwamanda.
Jim kadan bayan Kwamanda ya yi maganar ne, aka jiyo bullar faifan sautin wayar tarho tsakanin Ganduje da Ibrahim Masari, wanda tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa ne a jam’iyyar APC.
A cikin faifan sautin, an ji gwamnan yana kukan rashin adalci da shugaban kasa ya yi masa a ganawarsa da Kwankwaso.
Gwamnan ya fara tattaunawa ne da cewa ana ta hayaniya a duk fadin Kano kan ganawar da Tinubu da Kwankwaso suka yi.
Ganduje ya ce duk da Masari ya shaida masa yiwuwar gudanar da irin wannan taron, amma babu wani abu da zai iya yi a kai.













































