Rundunar Sojin Najeriya ta dauki alhakin harin da aka kai Jihar Kaduna

Chief of Army Staff Lt. Gen. Taoreed Lagbaja
Chief of Army Staff Lt. Gen. Taoreed Lagbaja

Rundunar sojin Najeriya ta dauki alhakin kai harin da aka kai ta sama na ranar Lahadi wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da dama a kauyen Tudun Biri da ke jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya tabbatar da hakan a karshen wani taron gaggawa na tsaro da aka gudanar a ranar Litinin.

Aruwan ya ce taron ya kasance karkashin jagorancin mataimakiyar gwamna, Dakta Hadiza Balarabe, wanda ya samu halartar shugabannin hukumomin tsaro da malaman addini da shugabannin gargajiya da kuma rundunar sojojin Najeriya.

Ya kara da cewa, “Babban Hafsan Sojan Najeriya shiyya ta daya, Manjo Janar Valentine Okoro ya bayyana cewa sojojin Najeriya na ci gaba da gudanar da ayyukansu na yaki da ‘yan ta’adda amma ba da gangan suka jefa Bam kan al’umma ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here