Ƙungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta ragargaza kungiyar Manchester City da ci 5-1 a gasar Firimiyar kasar Ingila.
Manchester City dake rike da kambun gasar ta yi rashin nasarar ne a filin wasa na Emirates mallakin Arsenal din a wasan mako 24 na gasar.
Nasarar da Arsenal din ta samu ya sanya ta kara matsar kungiyar Liverpool dake jan ragamar teburin gasar a matsayin ta 1 da maki 56 bayan da ta buga wasanni 23.
Kungiyar ta Arsenal ta fara zura kwallo ta hannun dan wasanta Kai Havertz mintuna biyu da sa wasa kafin daga bisani Erling Haaland ya warware kwallon a mintuna 55.
Ƙarin karatu: An saki magoya bayan Arsenal da aka kama kan wasansu da Manchester United
Sai kuma a mintuna na 56 T. Partey ya ci ta 2 sai kuma M. Lewis-Skelly ya zura ta 3 a mintuna na 62.
Kai Havertz ne ya ci ta hudu a mintuna 76 kafin daga bisani E. Nwaneri ya zura kwallo ta 5 a wasan.