Rundunar Sojin sama ta yi Karin girma ga jami’anta

edward
edward

Rundunar sojin sama, ta yi wa jami’anta 22 karin girma zuwa mukamin AVM, da kuma wasu 16 zuwa mukamin air Comodore.

Kamfanin dillancin labarai NAN ya rawaito cewa rundunar ta amince da karin girma ga Air Commodore 22 zuwa AVM da kuma Group Captain 16 zuwa Air Commodore.

Yayin bikin Karin girma ga jami’an a ranar juma’a, ministan tsaro, Muhammed Badaru, wanda ya samu wakilcin karamin minista, Bello Matawalle, ya bayyana cewa samun karin girma ga sojojin abin alfahari ne.

Ya ce karin girma da aka yi abu ne mai matukar burgewa, kuma mai matukar muhimmanci, da ya kamata a yi amfani da shi wajen wanzar da tsaro a kasar nan.

Ministan ya tunatar da jami’an cewa karin girman ya zo ne tare da kyakkyawan fata da nauyi gare su.

Ya yi kira a gare su da kada su manta da yakunan da ake yin da ta’addanci wajen ganin an samu zaman lafiya mai dorewa.

Karanta wannan: Wadanda suka kammala karatun digiri sun roki Gwamnatin Zamfara ta biya musu kudin shiga makarantar koyon aikin lauya

Badaru ya ce gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Bola Tinubu a tsaye take kyam wajen tallafawa sojojin Najeriya gaba daya.

Babban hafsan sojin sama, Air Marshal Hassan Abubakar, ya ce an karawa jami’an girma ne lura da kwazon su da kuma jajircewa a aiki.

AVM Suleiman Usman, daya daga cikin jami’an da aka kara wa girman ya yi magana a madadinsu.

Ya ce karin girman da suka samu wani kaimi ne a gare su wajen yi wa kasa hidima.

Usman ya ce suna sane da irin matsalolin tsaro dake addabar kasar nan, wandanda ake sa ran su magance su.

Ya kuma ba da tabbacin cewa za su bayar da gudunmawarsu a fannoni daban-daban, domin samar da dawwamammen zaman lafiya a cikin al’umma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here