Gwamna Radda ya dakatar da jami’i bisa zarginsa da sayar da gandun daji

Gov Radda
Gov Radda

Gwamnatin jihar Katsina ta bayar da umarnin dakatar da shugaban sashin kula da gandun daji na karamar hukumar Malumfashi da ke jihar nan take.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labaran Gwamnan, Alhaji Aliyu Yaradua ya sanya wa hannu a madadin Sakataren Gwamnatin Jihar.

Sanarwar ta ce hakan ya biyo bayan zargin shugaban na sayar da sassan dajin Makaurachi da ke yankin karamar hukumar.

Karanta wannan: Rundunar Sojin sama ta yi Karin girma ga jami’anta

Gwamna Dikko Radda ya kuma umarci hukumar karamar hukumar da ta zakulo duk wasu jami’an da ke da hannu a cikin wannan badakala.

Sanarwar ta kara da cewa, “Sunan Usman Illiyasu ya yi fice a cikin haramtattun harkalloli.

An kuma umarci hukumar karamar hukumar da ta yi bincike tare da kai rahoto ga gwamnan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here