NPFL: Pillars ta yi Allah wadai da farmakin da aka yiwa Katsina United a Kano

images 1 1 480x381 1
images 1 1 480x381 1

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars (Sai Masu Gida) ta yi Allah wadai da yadda wasu bata gari da sunan magoya bayanta suka farmaki ‘yan wasan Katsina United, a wasan mako 23 na gasar Firimiyar Najeriya ta kakar wasannin shekarar 2021/2022, a filin wasa na Sani Abacha dake kofar Mata a Kano.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa mutanen da ake zargin magoya bayan tawagar Kano Pillars ne, sun fara jefe-jefe ne tun a mintina na 82 da fara wasa tsakanin tawagogin biyu, sun kuma farfasa motar yan wasan Katsina United tare da kwashe musu muhimman abubuwan dake cikin motar, a ranar Asabar.

Wannan dai shi ne karon farko da Kano Pillars din ta dawo wasa buga wasa a filinta bayan shafe sama da shekaru biyu bata buga wasa a filin.

Kamar yadda rahoton ni suka nuna cewa sama da shekaru 20 kenan idan kungiyoyin za su buga wasa ba a wanyewa lafiya, ko da kuwa a gidan kowacce tawagar ce.

A sanarwar da jami’in yada labaran Kano Pillars Lurwanu Idris Malikawa Garu, ya fitar, yace an dakatar da wasan ne sakamakon hargitsi wasu batagarin magoya bayan kungiyar suka tayar, ta hanyar jefa ruwan Leda da wasu abubuwan daban zuwa cikin filin wasan, lamarin da ya sanya jami’an gudanar da gasar guduwa cikin dakin canja kayan ‘Yan wasa.

Sanarwar tace baya ga Motar kungiyar Katsina United da bata garin suka lalata sun kuma lalata wani bangare na Motar Kungiyar Kano Pillars ma.

Sanarwar ta kara da cewa basu yi tunanin irin wannan mummunan abu zai faru a yayin wasan ba, la’akhari da yadda a baya-bayan nan suka buga har kusan wasanni uku a filin wasa na Muhammad Dikko dake Katsina batare da wata matsala ba.

Ta kara da cewa mahukunta da masu ruwa da tsaki a kungiyar ta Kano Pillars ba zasu nade hannu su zuba ido irin haka tana faruwa ba kuma zasu dauki matakin shari’a akan duk wanda aka samu da hannu a cikin wannan hatsaniyar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here