Rashin wutar lantarki: Kasuwar masu cajin waya ta kara budewa

phone charging 1 700x430

Sakamakon katsewar wutar lantarki  a wasu sassan Najeriya da suka hada da Jos, wuraren cajin waya a cikin garin da kewaye suna ta samun karuwar yawan jama’a.

Wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, wanda ya ziyarci wasu cibiyoyin cajin, ya ruwaito cewa mazauna yankin sun yi dandazo da lambarsu domin yin cajin wayoyinsu.

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito cewa kamfanin na ‘Transmission Company of Nigeria’ (TCN),  ya ce ana kokarin gyara matsalar.

Yawancin masu irin waɗannan wuraren caji galibi suna sayar da kayan haɗin waya

Mista John Greg, wanda wurin cajinsa yake a unguwar Tudun Wada da ke karamar hukumar Jos ta Arewa (LGA) ta Filato, ya ce matsalar wutar lantarki ta kara yawan jama’a.

‘’Kamar yadda kuke gani, ina sayar da kayan aikin waya kuma ina cajin waya ga wadanda ba su da wutar lantarki kwata-kwata.

‘’Amma da rashin wutar lantarki da ake fama da shi a halin yanzu ya shafi yawancin jihohin arewa, Ina cajin wayoyi sama da 700 a kullum.

‘’A da a baya na kan caji kowace waya akan Naira 100, amma da yake mu ma muna amfani da janareta da kuma karin farashin man fetur, mun kuma kara farashin ayyukan mu zuwa Naira 200 a kowace waya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here