Rundunar ‘yan sandan ta cafke dan majalisar wakilai bisa kalaman batanci ga babban sufeton ‘yan sanda.
Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta cafke dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Aba ta Arewa da kuma Kudancin jihar Abia a majalisar wakilai, Hon. Alexander Ikwegh da laifin cin zarafin wani direban Bolt mai suna Mista Stephen Abuwatseya da kuma yin kalaman batanci a ofishin babban sufeton ‘yan sanda.
Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ya fitar a ranar Litinin, ta ce rundunar ta samu rahoto a hedikwatar Maitama, dangane da wani lamari da ya shafi Mista Abuwatseya da Hon. Alexander Ikwegh.