Gwamna Namadi ya sanya hannu kan kasafin kudin shekarar 2024

A 1
A 1

Gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi, ya sanya hannun kan kwarya-kwaryar kasafin kudin shekarar 2024 da ya kai Naira biliyan 298 da miliyan 140.

A 5, Namadi
Gwamna Namadi lokacin da yake sanya hannu

Sanya hannun gwamnan na zuwa ne mako guda bayan da kasafin ya tsallake karatu na 3 a majalisar dokokin jihar.

Karanta wannan: Yan sandan Kano sun kama mutum 9 bisa zargin cinikin Yara

Ya bayyana cewa kyakkyawar alakar dake tsakanin bangaren zartarwa da kuma su ‘yan majalisar shi ne ya bada damar kammala kasafin ba tare da wata lacuna ba.

A 3
Namadi yayin sanya hannu kan kasafin kudi

A 4

A cewarsa kwarya-kwaryan kasafin kudin an tsara shi ne ta yadda zai amfani al’ummar jihar Jigawa.

Karanta wannan: Shugaban karamar hukuma ya mutu a jihar Kebbi

Namadi ya kuma bukaci masu ruwa da tsaki da su bibiyi yadda za’a yi amfani da kasafin don ganin al’umma sun amfana yadda ya kamata.

Kamfanin dillancin labarai NAN ya rawaito cewa wadanda suka halarci bikin sanya hannu akan kasafin, sun hada da shugaban majalisar jiha Haruna Aliyu, da shugabannin kananan hukumomi da sauran manyan jami’an gwamnati.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here