Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu mutum 9 da suka kware a safarar mutane da garkuwa da kuma saye da sayarwa kananan Yara.
Kwamishinan ‘yan sandan Kano Muhammad Hussain Gumel, ne ya bayyana hakan ranar Alhamis lokacin da yake holin wadanda ake zargin a Shelkwatar rundunar dake Bompai.
Yace an kama mutanen ne a yankunan jihohin Kano da Bauchi da Gombe da Lagos da Delta da Anambra da kuma Imo.
Karanta wannan: Shugaban karamar hukuma ya mutu a jihar Kebbi
Acewar Gumel rundunar ta kuma kubutar da wadanda aka sace su 7.
Kwamishinan ya kuma ce daga cikin yaran da aka sayar dake tsakanin shekara 3 zuwa 7 an saida su ne akan Naira dubu 300 da Naira dubu 600.