Rundunar ‘Yan sandan Kano ta kama wani matashi Yusuf Haruna daga karamar hukumar Dala bisa zarginsa da kashe wani limami ta hanyar daba masa wuka.
Mai Magana da yawun rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
Karanta wannan: ‘Yan sanda sun kama matashin da ake zargi ya yi wa ƴar’uwarsa ciki kuma ta mutu
Sanarwar tace matashin ya daba wa limamin mai suna Mallam Sani Mohammed Shuaibu wukar ne a bayansa lokacin da yake alwala.
A cewar sanarwar, an garzaya da limamin asibitin kwararru na Murtala Muhammad inda kuma likita ya tabbatar da mutuwarsa sakamakon raunin da ya ji.
Karanta wannan: ‘Yan ta’adda sun kara kaiwa hari wasu yankunan Plateau
Sanarwar ta bayyana cewa matashin ya yi aika-aikar ne saboda yadda limamin ya sha gargadinsa da ƴan tawagarsa kan su daina busa tabar wiwi a harabar masallaci.
Runudnar ta ce za ta gudanar da bincike kan laifin domin tabbatar da adalci.