NBC ta ci tarar gidan talabijin na Arise bisa yada labaran karya kan Tinubu

NBC
NBC

Hukumar kulada kafafen labarai ta kasa ta dorawa gidan Talabijin na Arise TV tarar Naira miliyan biyu bisa zargin yada rahotonnin karya da suka saba ka’idojin yada labaran Najeriya.

A karshen makon nan ne dai aka samu rahotannin da ke cewa Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa na binciken shari’ar da ta shafi Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a kasar Amurka.

Sai dai hukumar zabe ta musanta wannan ikirarin, inda ta bayyana wata takarda da ke yawo wanda ke dauke da hujjoji tare da wasu bayanan da ake zargin Tinubu da dillacin kwayoyi a amurka a matsayin “karya”.

Da take maida martani, kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar APC ya bukaci NBC da ta sanyawa kafafen yada labaran da suka yada rahoton takunkumi.

A ranar Litinin din da ta gabata ne babban daraktan hukumar NBC Malam Shehu Illelah ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

“A ranar Asabar 12 ga watan Nuwamba, hukumar ta bibiyi yadda aka yi amfani da sanarwar manema labarai da aka ce Mista Festus Okoye, kwamishinan labarai na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ya fitar, inda tashar Arise TV ta yada.

“Sanarwar da aka rabawa manema labarai ta yi zargin cewa hukumar zabe na gudanar da bincike kan batun sharia da wata kotun Amurka ta yi kan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, da nufin gurfanar da shi a gaban kotu.

“Hukumar zaben ta yi watsi da sanarwar, inda tace babu kamshin gaskiya kan yadda ake alakanta sanarwar ga hukumar, karya ce zalla”

Idan za a iya tunawa, Illelah a tsakanin ranakun 19 zuwa 26 ga Satumba, 2022, ya karade kasar nan domin wayar da kan masu yada labarai tare da tunatar da su tanadin kundin tsarin yada labarai na Najeriya da kuma dokar zabe yayin da kasar ke dab da babban zabe na 2023.

Illelah ya ce hukumar tare da masu ruwa da tsaki sun dukufa wajen ganin an gudanar da zabukan 2023 cikin gaskiya da adalci, ya kuma bukaci kafafen labarai da su ci gaba da gudanar da ayyukansu cikin kwarewa, domin a samu nasarar gudanar da tsarin dimokuradiyya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here