Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta kori tsohon Ministan Neja Delta Godswill Akpabio daga tsayawa takarar Sanatan Akwa-Ibom ta arewa maso yamma na jam’iyyar APC a babban zaben 2023.
Wani kwamitin alkalai uku da mai shari’a Danlami Senchi ya karanta a ranar Litinin ya bayyana cewa Akpabio ya gaza gabatar da kwararan hujjoji cikin lokacin da doka ta tanada.
Kwamitin ya kuma yanke hukuncin cewa Akpabio, kasancewar sa dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, ba zai iya shiga zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar a ranar 27 ga watan Mayu ba, wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta sanyawa ido, wadda ta fitar da Udom Ekpoudom a matsayin dan takara.
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar 22 ga watan Satumba ta bukaci INEC ta mayar da Sanata Akpabio a matsayin dan takarar APC, a matsayin dan takarar da jam’iyyar ta tsayar a zaben fidda gwani na biyu na ranar 9 ga watan Yuni.
A baya dai kotun tarayyara ta bayar da umarnin cewa INEC ta karbi sunan tsohon Ministan a matsayin dan takarar jam’iyyar APC.
Mai shari’a Emeka Nwite wanda ya yanke hukuncin ya ce Akpabio ya samu nasarar tsayar da shi a matsayin dan takarar Sanatan Akwa-Ibom ta Arewa maso yamma na jam’iyyar APC daga zaben fidda gwani da kwamitin ayyuka na jam’iyyar ya gudanar a ranar 9 ga watan Yuni, 2022.
Alkalin kotun ya zargi INEC bisa sake gudanar da zaben fidda gwani baya ga na ranar 27 ga watan Mayu, wanda wani bangare na jam’iyyar karkashin jagorancin Augustine Ekanem ya gudanar da zaben fidda gwani na ranar 9 ga watan Yuni.













































