Kotu ta bawa Emefiele izinin fita daga Abuja

emefiele
emefiele

Babbar Kotun Tarayya da ke zaman ta a Abuja ta bawa tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele, izinin fita daga yankin Babban Birnin Tarayya.

A ranar Alhamis kotun ta ba da izinin bayan bukatar hakan da lauyan Emefiele, Mathew Bukka, SAN ya gabatar, yana neman ta sauya sharuddan belinsa da ta bayar.

Karanta wannan: Barkewar annobar Kwalara a Zambiya ta kashe Mutane sama da 400

A ranar 23 ga Nuwambar 2023 ne Mai Shari’a Hamza Mu’azu ya ba da belin Emefiele, wanda Hukumar yaki da masu karya tattalin arzikin kasa EFCC ta gurfanar kan zargin badakalar biliyoyin kudade a lokacin shugabancinsa na CBN.

A lokacin, Mai Shari’a Hamza Mu’azu ya shardanta wa Emefiele ajiye kudi Naira miliyan 300 da kuma kawo mutum biyu wadanda kowannensu ya mallaki gida a unguwar Maitama a Abuja su tsaya masa.

Haka kuma alkalin ya shardanta wa tsohon gwamnan na CBN cewa ba zai fita daga Abuja zuwa wani waje ba.

Karanta wannan: Cece-kuce: Kan kyautar motar Naira Miliyan 6 da Jaruma Fatima Hussaini ta samu

Amma a zaman ranar Alhamis, lauyansa, Matthew Bukka ya bakaci a janye sharadin hana shi fita daga Abuja, yana mai cewa a matsayin Emefiele na babban mutum ba zai tsere ba idan aka yi masa sassaucin fita daga Abuja.

Lauyan ya kara da cewa hasali ma takardunsa na tafiye-tafiye suna hannun kotu don haka babu halin ya tsere.

Lauyan hukumar EFCC Rotimi Oyedepo SAN, bai kalubanci bakutar lauyan na Emefiele ba, amma ya ce, “Duk da cewa takardun nasa suna hannun kotu, amma ya kamata ya rubuta alkawarin cewa ba zai bar Najeriya ba har sai an kammala shari’arsa.

Karanta wannan: Barazanar ‘yan bindiga ta tilasta mutanen kauyukan Zamfara 10 tserewa

“Wannan ba yana nufin cewa ina zargin zai iya tserewa ba,” in ji Oyedepo.

Ya kara da cewa,“an sha samun wadanda takardunsu na tafiye-tafiye ke hannun kotun sun tsere daga Najeriya, inda suke zuwa su ba da takardar rantsuwar karya cewa takardun nasu sun bace.”

Bayan sauraron bangarorin, alkalin ya sahale wa Emefiele fita daga Abuja, bisa sharadin ya kasance a cikin Najeriya har sai an kammala shari’ar.

“Kotu ta amince da bukatar wanda ake zargi. Amma wajibi ne ya kasance a Najeriya har sai an kammala shari’arsa,” in ji alkalin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here