Barazanar ‘yan bindiga ta tilasta mutanen kauyukan Zamfara 10 tserewa

hoton 'yan zamfara
hoton 'yan zamfara

Al’ummomin kauyuka 10 a karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara sun tsere daga matsugunan su saboda fargabar yiwuwar kai musu hari bayan barazanar da wani jagoran ‘yan bindiga na yankin Dan Nagala ya aike musu.

Rahotanni sun ce kauyukan da zuwa yanzu mutanensa suka tsere daga matsugunansu sun hada da Gidan Soro da Maje da Fanda Hakki baya ga Hayin Dankaro da kuma Doka da Dan Gamji sai Galmuwar Hannu da Dan Katsina sannan Dakwalge da kuma Gidan Arne.

Karanta wannan: FEC ta amince da sama da Naira Biliyan 9.6 don inganta rayuwar ma’aikata

Gargadin ‘yan bindigar ga al’ummomin kauyukan 10 na zuwa ne bayan luguden wutar da sojojin Najeriya da ke karkashin Operation Hadarin Daji suka yi musu a maboyarsu da ke cikin dajin Danbassa-Buzaya.

Yayin sumamen dakarun Sojin Najeriyar, sun gano shanu da ‘yan bindigar karkashin jagorancin Dan Nagala suka sace daga hannun daidaikun jama’a.

Karanta wannan: Ɗan Majalisar Tarayya ya rabawa mutum 7 tallafin karatu Naira Dubu 250,000 ga duk mutum ɗaya

Wani mazaunin kauyen Gidan Soro ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa tun bayan da sojojin Najeriya suka kai sumame dajin tare da kwashe shanun dan bindigar ne makwanni 3 da suka gabata ne Dan Nagala ya aike da sakon gargadin cewa sai ya kai hari ilahirin kauyukan da ke kewaye da dajin.

A cewar rahotanni wannan dalili ya sanya al’ummomin kauyukan tserewa don kare rayukansu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here