Ba makiyaya muka kashe a hari ta sama a Nasarawa ba – NAF

795c775a 0f1b 40f4 b0aa 916ea2b39de0
795c775a 0f1b 40f4 b0aa 916ea2b39de0

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce mutum 38 da ta kashe a lokacin wani hari ta sama cikin watan Janairu a garin Rukubi da ke ƙaramar hukumar Doma a jihar Nasarawa ‘yan ta’addana ne ba ‘makiyaya’ ba kamar yadda ake zargi.

Mai magana da yawun rundunar Air Commodore Ayodele Famuyiwa, ne ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja babban birnin ƙasar jim kaɗan bayan taron manema labarai da rundunar ke gudanarwar duk bayan mako biyu a shalkwatar hukumar tsaron ƙasar.

Mista Famuyiwa ya ce ‘yan ta’adda ne dakarun sojin saman suka kashe, kuma rundunar ta ƙaddamar da harin ne bayan da suka samu bayanan sirri kan ayyukan ‘yan ta’addan.

A cinin watan Janairu ne aka ƙaddamar da harin tare da kashe mutanen a garin Rukubi a lokacin da suke komawa jihar daga makwabciyarta Benue.

A makon da ya gabata ne ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Humar Right Watch ta fitar da wani rahoto da a ciki ta zargi rundunar sojin saman Najeriyar da rashin bayar da cikakken bayani kan harin.

Human Rights Watch ta ce ta yi nazari tare da tantance wasu hotuna guda takwas da ke nuna wasu gawarwakin, sannan a ranar 14 ga watan Maris ta ziyarci wani kabari da aka binne gawarwaki 31.

A ranar 3 ga watan Mayu ne kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta rubuta wa babban hafsan hafsoshin sojin sama na Najeriya, wanda ke kula da rundunar sojin sama da ke gudanar da ayyukan soji, da kuma babban hafsan tsaron da ke kula da dukkan rundunonin soji ciki har da na sojojin sama, domin su bayar da cikakkun bayanai.

Kungiyar ta kuma bayyana jinkirin da rundunar sojin saman ke yi a matsayin abin da ba a lamunta ba, inda ta buƙaci a gaggauta gudanar da bincike mai zaman kansa kan lamarin.

Haka kuma HRW ta buƙaci rundunar sojin saman ta biya diyya ga iyalan waɗanda suka mutu a lokacin harin.

Ita ma ƙungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) mai kare muradun makiyaya a ƙasar ta zargi sojojin da kisan makiyayan da ba su ba kuma ba su gani a a lokacin hari.

To sai dai Mista Famuyiwa ya kalubalanci ƙungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) da duk masu ikirarin cewa an kashe makiyaya a da shanu a lokacin harin da su bayyana wa duniya hujjarsu domin tabbatar da ikirarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here