
Ma’aikatar lafiya ta Hamas ta ce mutum sittin da bakwai aka kashe a hare-haren da aka kai cikin dare kan Rafah, kamar yadda kakakin kungiyar Asharf Al-Qudra ya bayyana.
Akwai rahotanni mabanbanta kan adadin mutanen da hare-haren na Isra’ila suka kashe.
Karanta wannan: Ma’aikatan jinya da ungozoma na zanga-zanga a Abuja
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce adadin mutanen da suka mutu sun kai kusan mutane 100 inda ta rawaito ma’aikatar lafiya ta Hamas ke fada.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake samun tashe-tashen hankula a wasu kasashe na duniya ba.