Sallah: Dalilan da suka sa sarkin Kano na 15 Aminu Ado ya soke hawan sallah

Alhaji Aminu Ado Bayero (1)

Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya sanar da soke duk wasu shirye-shiryen gudanar da bikin hawan sallah da ake gudanarwa duk shekara kamar yadda aka tsara da farko.

Aminu Ado Bayero ya bayyana hakan ne a cikin wani dan takaitaccen faifan bidiyo da yammacin jiya Laraba, inda ya bayyana dalilan da suka sa aka dakatar da shirin hawan.

Sarkin Bayero ya bayyana a cikin faifan bidiyon cewa ya soke bikin hawan ne saboda kokarin da malaman addinin Musulunci da ake girmamawa da kuma dattawa suka yi wajen ganin an samu zaman lafiya.

“Dole ne mu dakatar da shirin gudanar da wannan al’amari bayan da malaman addinin Musulunci masu daraja da kuma dattawa suka yi galaba a kanmu, bayan tattaunawa da mashawarta na,” inji Aminu Bayero.

‘’Bikin hawa ba wai a yi ko a mutu ba ne, domin zaman lafiyar jama’a ya fi komai muhimmanci a gare mu.

Ya kuma yi kira ga mazauna garin Kano da su yi amfani da wannan biki wajen ziyartar iyalai da abokan arziki tare da addu’ar Allah ya kara zaman lafiya a jihar da ma Najeriya baki daya.

SolaceBase ta ruwaito cewa, Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, tun da farko ya sanar da jami’an tsaro shirinsa na gudanar da hawan a lokacin bikin Eid-el-Fitr.

Haka kuma, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umarci mai martaba Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II tare da sauran sarakuna da su shirya bikin hawan na shekara-shekara domin tunawa da bukukuwan karamar Sallah.

Hakan dai ya haifar da fargabar tashin hankali da kuma tabarbarewar tsaro a birnin Kano, lamarin da ya sa ‘yan sanda suka bawa jama’a tabbacin kare rayuka da dukiyoyin su kafin bukukuwan Sallah da kuma bayan bukukuwan Sallah.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here