Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta shiga yajin aikin da kungiyoyin kwadagon da suka hada da Kungiyar Kwadago ta Najeriya da kuma Kungiyar Kwadago ke yi.
Hakan na zuwa ne bayan da gwamnatin tarayya ta gaza biyan mafi karancin albashin ma’aikata.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar, Emmanuel Osodeke, ya aike wa shugabannin reshe da kuma ko’odinetocin shiyyar na ASUU a ranar Litinin, ya umarci malaman jami’o’in kasar nan da su shiga yajin aikin a matsayin na kungiyar.
Karin labari: NLC: Najeriya ta shiga cikin wani sabon yanayi sakamakon yajin aikin kungiyar Kwadago
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Kungiyar NLC ta sanar da fara yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar Litinin 3 ga watan Yuni 2024, sakamakon gazawar da gwamnati ta yi na kammala sasantawa kan batun biyan mafi karancin albashi ga ma’aikatan Najeriya da kuma sauya farashin wutar lantarki.
“An umarci rassan mu da su shiga yajin aikin a matsayin nuna goyon baya.
“Saboda haka, shugabannin reshe za su hada dukkan mambobin kungiyar don shiga yajin aikin cikin gwagwarmaya.”
Karin labari: Yanzu-yanzu: CBN ya soke lasisin bankin Heritage
Idan dai za a iya tunawa ASUU ta dade tana tunanin shiga yajin aikin ne bayan ta yi Allah wadai da gazawar da gwamnatin tarayya ta yi na nada majalisar gudanarwar jami’o’in tarayya.
Kungiyar ta kuma yi Allah wadai da abin da ta bayyana a matsayin rashin da’a na gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Tinubu kan al’amuran da suka shafi malaman jami’o’in tarayyar Najeriya.