Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya soke lasisin bankin Heritage ba tare da bata lokaci ba.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa a ranar Litinin da ta gabata ta hannun mukaddashin daraktan sadarwa na bankin CBN, Hakama Sidi Ali.
Sanarwar ta ce matakin ya zama dole saboda sabawa sashe na 12 (1) na dokar BOFIA, 2020 da bankin ya yi.
Ya ce: “Hukumar gudanarwa na bankin ba su iya inganta harkokin kudi na bankin ba, lamarin da ke zama barazana ga daidaiton kudi.
Karin labari: Hukumar NDLEA ta kama miyagun kwayoyi da suka kai na Sama da Naira Biliyan 2.1
“Wannan ya biyo bayan lokacin da CBN ya yi hulda da bankin tare da tsara matakai daban-daban da nufin dakile koma baya.
“Abin takaici, bankin ya ci gaba da shan wahala kuma ba shi da kyakkyawan fata na farfadowa, wanda hakan ya sa soke lasisin ya zama mataki na gaba.
A cewar sanarwar, CBN ya dauki wannan mataki ne domin karfafa kwarin gwiwa da jama’a kan harkokin banki da kuma tabbatar da cewa ba a tauye tsarin hada-hadar kudi ba.
Karin labari: ASUU ta dakatar da yajin aikin gargadi na makonni biyu a Kano
Sanarwar ta ce, “Muna so mu tabbatarwa jama’a cewa tsarin hada-hadar kudi na Najeriya ya ci gaba da kasancewa a kan turba.
“Matakin da muke dauka a yau ya nuna yadda muke ci gaba da daukar dukkan matakan da suka dace don tabbatar da tsaro da ingancin tsarin hada-hadar kudi.”