Shugaban riko na gwamnatin jihar Rivers vice admiral Ibok Ete Ibas mai ritaya ya gurfana a gaban kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai, bayan an sha ɗage zaman.
Majalisar na amfani da ‘yancin da kundin tsarin mulkin kasar ya ba ta na bincikar ayyukan majalisar dokokin jihar Rivers.
Ibas ya nemi afuwar kwamitin kan rashin halartar taron a lokutan da aka rika sanyawa, inda ya kuma bukaci a ba shi karin lokaci domin shiryawa kwamitin bayani.
Ya ce har yanzu yana nan yana shiri tsara yadda aikin sa na rikon shugabancin jihar zai gudana, kafin ya kai ga fahimtar da kwamitin.
Bayan rokon da ya yi wa kwamitin, an ba ‘yan jarida uzuri, kuma taron ya shiga wani zama na sirri.
Karin karatu: Gwamna Kano ya rattaba hannu kan dokar kafa sabbin hukumomi 4
Da aka kammala taron bayan kimanin awa daya, Ibas mai ritaya ya tafi ba tare da cewa komai ba.
A makon jiya ne kwamitin majalisar ya sake dage zaman tattaunawa da Ibas.
A cewar sanarwar da ta sanar da dage taron, sauyin lokaci ya biyo bayan bukatar da Ibas ya gabatar a hukumance.
Gwamnan na Rivers yana cikin gwamnonin jihohin da suka halarci taron majalisar tattalin Arzikin ƙasa (NEC) a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Alhamis.
Ibas ya fara fitowa ne a taron NEC bayan shugaban kasa Bola Tinubu ya nada shi a matsayin mai kula da jihar Rivers shi kadai bayan dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara a watan Maris din 2025.
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ne ya jagoranci taron wanda ya samu halartar gwamnoni da dama da wasu mataimakan gwamnoni daga jihohin kasar nan 36.