Mutane 50 sun mutu bayan nutsewar kwale-kwalensu a Congo

hatsarin, jirgin ruwa, mutu, congo, kwale-kwale
Ana fargabar mutuwar fasinjoji 10 da wani karamin jirgin ruwa mai dauke da mutane 50 da ya nutse a ruwan yankin gabashin lardin Kivu na Jamhuriyyar...

Ana fargabar mutuwar fasinjoji 10 da wani karamin jirgin ruwa mai dauke da mutane 50 da ya nutse a ruwan yankin gabashin lardin Kivu na Jamhuriyyar demokradiyyar Congo.

Mahukuntan yankin sun ce har zuwa wayewar garin yau Laraba an ci gaba da aikin laluben gawarwakin fasinjan jirgin amma ba a kai ga iya nasarar gano ilahirin su ba.

Karanta wannan: Kotun Ghana ta yi wa wasu mutum 12 daurin rai da rai kan kisan Soja

Mustafa Mamboleo babban jami’in yankin ya shaidawa manema labarai cewa an yi nasarar ceto mutum 10 da ransu sai kuma gawarwaki 3 da aka iya tsamowa daga ruwa.

A cewarsa akwai sauran mutum akalla 37 da ake kyautata zaton sun mutu a cikin ruwan, yayin ibtila’in wanda ya faru tun a daren Lahadin da ta gabata.

Rahotanni sun ce karamin jirgin ruwan ya yi lodin da ya wuce kima ne bayan daukar akalla fasinja 50 da kuma buhun siminti 20.

Karanta wannan: Gwamna Adeleke ya sanya dokar hana fita bayan mutuwar mutum 2 a rikicin Jihar Osun

Matsalar hadarin kwale-kwale ko kuma kananun jiragen ruwa da akan yi da katako ba sabon abu ba ne a jamhuriyyar Congo inda ko a watan jiya wasu mutum 22 suka mutu a Mai-Ndombe bayan nutsewar kwale-kwalensu a ruwa.

Haka zalika ko cikin watan Aprilun bara sai da makamancin hadarin kwale-kwalen ya kashe mutane 6 wasu 64 kuma suka bace a ruwan tafkin Kivu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here