Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ba da umarni ga Hukumar kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) da ta gaggauta rage kuɗin aikin Hajjin shekarar 2026 da ta sanar a baya-bayan nan.
Mataimakin Shugaban Ma’aikata na Fadar Shugaban Ƙasa, Sanata Ibrahim Hadeija, ne ya bayyana haka bayan wani taro da jami’an NAHCON a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa hukumar ta sanar da sabbin kuɗin aikin hajji bayan yin shawara da manyan masu ruwa da tsaki, inda masu tafiya daga yankin Maiduguri–Yola (Jihar Yobe, Borno, Adamawa da Taraba) za su biya naira miliyan 8.318, yayin da na jihohin Arewa za su biya naira miliyan 8.244, sai kuma na Kudanci su biya naira miliyan 8.561.
Sai dai Hadeija ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya ga buƙatar sake duba yiwuwar rage waɗannan kuɗaɗe, ganin yadda tattalin arziki ke samun ɗan ci gaba.
Ya ce yawancin kuɗin aikin hajji kusan kaso 95 cikin ɗari kuɗin kasashen waje ne, kuma an lissafa su ne bisa farashin canji na naira 1,550, wanda yanzu ya inganta.
Karin labari: NAHCON ta samu rangwamen Naira biliyan 19 don aikin Hajjin 2026
Hadeija ya ƙara da cewa idan a bara mahajjata sun biya tsakanin naira miliyan 8.5 zuwa 8.6 bisa farashin canji mara kyau, yanzu da naira ke ƙara ƙarfi, kamata ya yi a sauƙaƙa musu.
Ya ce idan an yi amfani da sabon ƙimar musayar kuɗi, akwai yiwuwar rage kuɗin zuwa tsakanin naira miliyan 7.6 zuwa 7.7, kuma za a sanar da adadin ƙarshe cikin kwanaki biyu.
Ya kuma yi gargadin cewa nasarar rage kuɗin na da alaƙa da saurin biyan kuɗin aikin hajji daga jihohi zuwa hukumar NAHCON domin ta samu damar siyan daloli daga Babban Bankin Najeriya (CBN) cikin lokaci.
A nasa bangaren, shugaban Hukumar Jin Dadin Mahajjata ta Jihar Kebbi, Alhaji Faruk Yaro, ya yaba da matakin gwamnatin tarayya bisa wannan mataki.
Haka kuma, Sakatare na NAHCON, Dakta Mustapha Mohammad, ya bayyana cewa matakin rage kuɗin aikin hajji zai bai wa karin Musulmi damar aiwatar da wannan rukuni na addini cikin sauƙi.












































