Wani bala’i ya afku a yau Talata yayin da shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Jigawa ta tsakiya Alhaji Isa Burji yanke jiki ya faɗi tmrai ya yi halinsa a wani otal da ke Abuja.
Shugaban jam’iyyar APC na Jigawa ta Gabas, Alhaji Abdullahi Ango ne ya bayyana haka ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN a dandalin Eagle Square da za a gudanar da babban taron jam’iyyar APC na ƙasa.
Ango ya ce, marigayin ya rasu ne da misalin karfe 3:30 na rana sa’o’i kaɗan kafin fara taron.
Ya bayyana cewa ya rasu ne kwatsam, inda ya kara da cewa, “Marigayin ya ci abincin rana kuma ya yi sallar la’asar gaba in rasuwar tasa.
“Ba shi da tarihin kowace irin cuta, Sai kawai ya fadi ya mutu nan take, inji shi.
Ango ya kuma ƙaryata wasu rahotonnin kafafen sada zumunta da ke cewa marigayin ya rasu ne a dandalin Eagle Square.
Ango ya bayyana marigayi Burji a matsayin mutumin kirki kuma mai gaskiya, shi ne jagoran tawagar Jigawa har ya rasu.
“Allah ya jikansa ya gafarta masa yasa Aljannar Firdausi ce makomarsa.”













































