Wakilan kungiyoyi masu zaman kan su dake aikace aikacen tabbatar da zaman lafiya da takwarorin su dake ayyukan kare hakin dan adam a matakin Najeriya da sassan Afrika ne suka halarci taro wadda ya wakana a jihar Kano.
Kazalika, wakilai daga sassan duniya da kuma ofisoshin diplomasiyya na wasu kasashe sun bada gudunmawa ga zauren taron ta kafar sadarwa ta internet.
Rawar da hukumomi da kungiyoyi da cibiyoyin gwamnati da ma daidaikun mutane ka iya takawa wajen wanzar da adalci da kare hakkin dan adam a kowane lokaci da nufin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’umomi sune batutuwan da suka mamaye ajandar taron.
Farfesa Buhari Isa, shi ne babban Jami’in gudanarwa a ofishin kula da kungiyoyin diplomasiyya dana kare hakkin dan adam na Afrika, ya fayyace ayyukan da suka sanya a gaba domin cimma manufa.
Ya ce suna ayyukan tabbatar da zaman lafiya da kare hakkin dan Adam da shirya bita akan mahimmancin adalci da kuma kyautatawa.
A yayin taron wadda wakilai daga kasashen Turai da nahiyar Asiya suka bada gudunmawa ta kafar Zoom, kungiyoyin kare ‘yancin Dan-Adam da na diplomasiyya da zaman lafiya hadin gwiwa da School of LEADERSHIP ta Amurka sun karrama Hajiya Hassan Saminu Turaki da lambar Jakadiyar wanzar da zaman lafiya bisa la’akari da kokarinta ta wannan fuska.
Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da hukumar kare hakkin Dan-Adam ta Najeriya ke cewa kunci da tsadar rayuwa a kasar na kara alkaluman cin zarafi da take hakkin bil’adama a tsakanin iyalai.
Ambasada Hajiya Hassana Saminu Turaki, ita ce mace ta farko a nahiyar Africa da ta samu irin wadannan lambobin yabo har guda 8 a matakin Duniya.
Lambobin Yabon masu mahimmanci daga Gabashin Turai, bisa fafutukarta ta gina al’umma da rayuwarsu don kare mutuncin kowane jinsin Dan-Adam, da kokarin samar da hadin kai da wanzar da zaman lafiya, tare da sulhunta al’umma, da karfafa tsarin zamantakewarsu, baya ga taimakawa mata su dogara da kansu.












































