Aƙalla mutane 100 ake fargabar sun mutu bayan rugujewar wani ramin hakar zinare a Jihar Zamfara, a cewar wasu da suka tsira daga hatsarin da mazauna yankin suka bayyana a ranar Juma’a.
Rahotanni sun nuna cewa ramin dake wurin hakar ma’adinai na Kadauri a ƙaramar hukumar Maru ya ruguje ne da daddare a ranar Alhamis, a lokacin da daruruwan ma’aikatan hakar zinare ke cikin ƙasa suna aiki.
Shaidun gani da ido sun shaida wa kamfanin dillancin labarai Reuters cewa lamarin ya auku ne yayin da ake ci gaba da aiki.
Wani mazaunin yankin mai suna Sanusi Auwal, wanda ya shiga aikin ceto, ya tabbatar da cewa an fito da gawarwaki 13 daga cikin ramin, ciki har da ta ɗan uwansa.
Ya ce, “Fiye da mutane 100 ne suka kasance a cikin ramin lokacin da ya ruguje.”
Haka kuma, babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Zamfara (ZSEMA), Ambasada Bala Ahmad, ya tabbatar da faruwar hatsarin a ranar Juma’a a Gusau.
Ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN cewa ramin ya rufta tare da hallakawa da kuma rufe ma’adinan gargajiya da yawa, amma bai bayar da ƙarin bayani ba.
Shugabannin al’umma a yankin sun bayyana wa kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ta wayar tarho cewa daruruwan mutane sun makale a cikin ramukan da suka rufta sakamakon ruwan sama mai yawa da aka tafka a yankin tun kafin faruwar lamarin.
Ƙarin labari: Gwamna Idris ya rufe wurin hakar zinare a Kebbi saboda tashin hankali
Sun ƙara da cewa ba a tantance adadin waɗanda suka mutu ko suka makale ba tukuna.
Sai dai sun tabbatar da cewa waɗanda suka samu raunuka ana kai su asibitin Maru domin kulawa.
A halin yanzu, al’ummar yankin tare da jami’an gwamnati na ci gaba da aikin ceto domin kubutar da waɗanda har yanzu ke makale a ƙarƙashin ramin da ya ruguje.
NAN












































