Wani babban farfesa a fannin koyar da aikin jarida a jami’ar jihar Legas (LASU), Lai Oso, ya kwanta dama. Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa, Farfesa Oso, mai shekara 67 a duniya, ya koma ga mahaliccinsa ne bayan wani mummunan hatsarin mota ya ritsa da shi a ranar Asabar.
Farfesan ya gamu da hatsarin ne lokacin da yake dawowa daga jami’ar jihar Delta (DELSU) da ke a Abraka, bayan ya halarci wani taro, rahoton The Punch ya tabbatar.
Lai Oso farfesa ne a makarantar koyon aikin jarida ta jami’ar jihar Legas (LASU).