Hukumar kula da jin daɗin alhazan jihar Kano ta fara wata ziyarar aiki a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya domin duba muhimman kayayyakin masauki da sufuri gabanin aikin Hajjin shekarar 2026.
Ziyarar na da nufin tantance yanayin wuraren kwana da tsarin jigilar alhazai, domin tabbatar da cewa an tanadi dukkan abubuwan da za su sauƙaƙa gudanar da aikin Hajji ga alhazan jihar Kano a bana.
Sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Suleiman Dederi, ya fitar a Kano, ta bayyana cewa Darakta Janar na hukumar, Alhaji Lamin Danbappa, tare da Shugaban hukumar, Alhaji Yusuf Lawan, ne suka jagoranci ziyarar duba kayayyakin.
Karanta: Ba za a bar Kwankwaso ya tsaya takara a jam’iyyar mu ba a 2027 ba – NNPP
Hukumar ta bayyana cewa manufar ziyarar ita ce tabbatar da jin daɗi, walwala da tsaron lafiyar alhazan Kano a lokacin aikin Hajji mai zuwa, tare da rage duk wata matsala da ka iya tasowa a lokacin ibada.
A yayin ziyarar, shugabannin hukumar sun duba wuraren masaukin alhazai a Makkah, sannan suka yi tattaunawa da Shugaban Hukumar Hajji ta ƙasa NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, domin ƙarfafa haɗin gwiwa da magance batutuwan gudanarwa.
Hukumar ta sake bayyana aniyarta na ci gaba da aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki, domin tabbatar da tafiyar da aikin Hajji cikin sauƙi da kwanciyar hankali, tare da bai wa alhazan Kano damar gudanar da ibadarsu yadda ya kamata cikin nutsuwa da cikar buri na ruhaniya.












































